Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Italiya ta ce an bindigar Nijeriya sun sako dan kasar


Shugaban Italiya Mario Monti da Shugaba Barack Obama na Amurka

ami’ai a kasar Italiya, sun bayyana cewar ‘yan bindigar Nigeriar nan da suka sace Injiniya dan Italiya Modesto di Girolamo, domin garkuwar dashi sun sako shi jiya Juma’a.

Jami’ai a kasar Italiya, sun bayyana cewar ‘yan bindigar Nigeriar nan da suka sace Injiniya dan Italiya Modesto di Girolamo, domin garkuwar dashi sun sako shi jiya Juma’a.

Injiniya Modesto yana yiwa kamafanin gine-ginen hanyoyi na Borini Prono aikin ginin hanyoyi ne a jihar Kwara-Nigeria. Kuma Ministan harkokin wajen Italiya, Giulio Terzi ya tabbatar da sahihancin rahoton sakin Injiniyan, yace harma an shaidawa iyalinsa halin da ake ciki.

Wasu ‘yan bindigar da ba’a tantance da manufarsu bane dauke da makamai suka sace Modesto di Girolamo domin yin garkuwa dashi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG