Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Ivory Coast Ta Kai Kara Switzerland Kan Dukiyar Da Gbagbo Ya Tara


Sabon shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara

Sabuwar gwamnatin Ivory Coast ta kai takardar koke a Switzerland ta karar Laurent Gbagbo, ta na neman a yi bincike game da kadarorin da ke kasar da ake danganta su da tsohon shugaban Ivory Coast.

Sabuwar gwamnatin Ivory Coast ta kai takardar koke a Switzerland ta karar Laurent Gbagbo, ta na neman a yi bincike game da kadarorin da ke wannan kasa ta tsaunuka da ake danganta su da tsohon shugaban Ivory Coast.

Wani lauyan Swizerland da ke kare gwamnatin Ivory Coast mai suna Bruno de Preux, an ruwaito yau Litini ya na cewa ya gabatar da takardar tuhumar Mr. Gbagbo, da matarsa da wasu mukarrabansa da dama.

A cikin watan Janairu, gwamnatin Swizerland ta kame kadarori masu tsadar kimanin kudi dala miliyan 81 da ake alakanta su da Gbagbo.

Jami’an gwamnati sun ce an kame kadarorin ne don a hana amfani da su har sai gwamnatin Ivory Coast ta tantance ko ta halaltacciyar hanya aka samu ko a’a.

Mr. Gbagbo ya cigaba da kasancewa cikin daurin talala a arewacin Ivory Coast bayan da aka kama shi a gidansa da ke Abidjan a makon jiya.

Tsohon shugaban ya ki mika ragamar iko bayan ya fadi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban da ya gabata wanda Alassane Ouattara ya ci.

Ran Jumma’ar da ta gabata ce aka rantsar da sabon shugaban da kasashen duniya su ka amince das hi, wanda hakan ya kawo karshen jina-jinan watannin hudu na jayayyar shugabanci tsakanin bangarorin biyu.

XS
SM
MD
LG