Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Jamus Na Taimakawa Wajen Samar Da Zaman Lafiya a Jihar Filato


n Bindiga Sun Kashe Mutane 37 a Jihar Filato, Nuwamba 26, 2013
n Bindiga Sun Kashe Mutane 37 a Jihar Filato, Nuwamba 26, 2013

Ganin yadda matsalolin tsaro suka addabi wasu sassan jihar Filato ya sa gwamnatin kasar Jamus ta yunkuro don taimakawa ta hanyar horas da shugabannin kungiyoyin al’umma.

A wani taron ‘karawa juna sani wanda ya hada da shugabannin addinai mata da matasa da makiyaya da kuma manoma daga ‘kananan hukumomi biyar da ake yawan samun tashin hankali da ma ‘yan jarida, domin tattaunawa kan musabbabin tashin rikici da ake samu a yankunan da kuma dabarun magancesu.

Mr Akin Omoware, jami’i ne dake aiki a hukumar inganta rayuwar al’umma ta kasar Jamus dake jihar Filato, ya shaidawa Muryar Amurka cewar manufar taron ita ce su ‘kara kwarin gwiwa wa hukumar sasantawa ta jihar Filato ta hanyar horas da masu ruwa da tsaki dabarun fahintar alamun dake haddasa rikici da hanyoyin magancesu ba tare da an samu tashin hankali ba.

Mr Akin, ya ce ba wanda ke amfana da tashin hankali, ko da ma mutum yana ganin kamar akwai ribar da yake samu a yanzu a rikicin dake aukuwa, tabbas watarana zai yi da na sani, saboda duk abin da mutum ya samu ta hanyar rikici, to kuwa ta hanyar rikicin zai rasa shi, don haka dole mu tabbatar mun sanya tubalin da zai taimaka wajen sasantawa da fahintar juna.

Daraktan labarai na gidan rediyo da talabijin mallakar jihar Pilato, Yakubu Tadi ya ce ‘yan Jarida nada gagarumin gudunmowa a harkar tsaro.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG