Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Kenya Tana Fuskantar Sake Barkewar Coronavirus


Ma'aikatan jinya na gwajin cutar COVID-19 a unguwar Kibera Nairobi, Kenya

Kasar Kenya na fuskantar barazanar zagaye na biyu na yaduwar cutar coronavirus inda alkalumar wadanda ke dauke da cutar ke kara hauhawa.

Kasar Kenya ta fara fuskantar sake barkewar coronavirus, bayan makwanni uku da ta dage wasu muhimman dokokin dakile yaduwar cutar.

Ministan kiwon lafiyar Kenya yayi kashedi a ranar Lahadi cewa kasar na cikin mawuyacin hali bayan da aka sanar da samun sababbin kamuwa 600 da mace mace da dama.

Wakilin Muryar Amurka a Nairobi yace masana sun ce akwai yiwuwar fuskantar kalubale idan aka sake kakaba dokokin hana zirga zirga.

Jami’an kiwon lafiya sun fargar da jama’a bayan da kasar ta samu sababbin kamuwa da cutar a cikin ‘yan makwanni da aka sassauta dokokin takaita yaduwar cutar.

Ministan kiwon lafiya Mutahi Kagwe yace mutum bakwai suka mutu da cutar a ranar Lahadi kana wasu 685 suka kamu da cutar a cikin kasar.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG