A jiya Laraba ne shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Koriya ta Arewa a matsayin “matsalar da dole sai anyi maganinta.”
A lokacin da shugaba yake tare da Faray Ministan Canada, Justin Trudeau, a ofishinsa dake fadar White House, Trump ya ce “Tabbas, zanyi abin da ya dace ga Amurka, da kuma abin da ya dace ga duniya baki daya.”
A halin yanzu kuma, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa, Ri Yong Ho,ya zargi shugaba Trump da cewa shine ya soma kunna wutar tsokanar janyo yaki a yankunan Koriya, bayan da yayi baraznar cewa Amurka zata ruguza Koriya ta Arewa idan har ta kai mata hari.
Trump dai yayi wannan barazanar ne a lokacin da yake jawabi a gaban babban taron shugabannin kasashen duniya a zauren MDD a watan da ya gabata.
A daidai lokacinda shugaban na Amurka ketunanin amfani da karfin soja kan Koriya ta Arewa, sojojin Amurka da Japan dana Koriya ta Kudu, sun gudanar da wani atisaye don tsoratar da Koriya ta Arewa, inda suka yi ta harba makamai masu linzami daga gabashi da kuma yammacin gabar zirin koriya a ranar Talatar shekaranjiya.
Facebook Forum