Accessibility links

Kasar Liberiya ta rufe kan iyakarta da Ivory Coast

  • Ibrahim Garba

Shugabannin Afirka a kokarinsu na neman mafita game da rigingimun yankin

Kasar Liberiya ta rufe kan iyakarta da kasar Ivory Coast, bayan da aka yi zargin

Kasar Liberiya ta rufe kan iyakarta da kasar Ivory Coast, bayan da aka yi zargin cewa wasu ‘yan bindiga sun ketara zuwa Ivory Coast su ka hallaka wasu dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Ministan yada labarai Lewis Brown ne ya bayar da sanarwar a yayin wani taron manema labarai a birnin Monrovia ranar Litini.

Ya ce Liberiya ta kuma tura sojoji da ‘yan sanda don su kare kan iyakar, ta kuma dakatar da duk wani aikin hako ma’adanai a wurin. Har yanzu hukumomi a Liberiya na binciken inda ‘yan bindigar su ke.

Jami’an gwamnmatin Ivory Cosat su k ace wasu ‘yan bindigar da ke da zama a kasar Liberiya ne su ka kashe dakarun tabbatar da zamann lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su 7 da kuma wasu fararen hula 8 a ranar Jumma’a a garin Tai da ke yammacin kasar, a kusa da kan iyakar kasashen biyu.

XS
SM
MD
LG