Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Mali Ta Tasa Keyar Wani Dan Taadda Zuwa Babban Kotun Kasa Da Kasa


Mahukunta a kasar Mali sun tsare dan taaddan kasar Al Hassan Abdulazeez Mohammed doomin ya fuskaci sharaar ayyukan taaddanci

Jiya asabar ne aka tsare wani dan jihadin kasar Mali kuma tuni aka mika shi ga babban kotun nan mai binciken manya laifuka ta kasa-da-kasa domin ya fuskanci tuhumar laifin yaki tare da wargaza wurin ibada aTimbuktu da kuma fyade.

Mahukuntar kasar dai ta Mali ne suka tsare al-Hassan Abdul Azeez Mohammed Mahamond, kuma yanzu haka ya isa inda ake ajiye masu jiran sharia dake birnin Hague.

Shi dai wannan mutumin dan shekaru 40 a haihuwa ya jima da zama dan kungiyar al-qaida wanda shine ma babban dan sandar kungiyar daga watan afirilu na 2012 zuwa watan janairu na shekarar 2013.

Daga cikin tuhumu-tuhumen da zai fuskanta ko sun hada da laifin yaki,tursasawa wa bil adama da kuma wargaza wurin ibadah dake Timbuktu sai fyade da kuma tilasta mata auren dole.

An zargi Hassan da hannu dumu-dumu cikin samar da shirin auren dole, wanda hakan ya takura wa ‘yan mata dake wannan yankin Timbuktu sai kuma yawaita fyade da tura mata karuwanci bada sonsu ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG