Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Malta Ta Amincewa Jirgin Bakin Haure Ya Shiga Tashar Tekunta


Bakin haure cikin jirgin dake dauke dasu
Bakin haure cikin jirgin dake dauke dasu

Bayan da farko ta ki amincewa jirgin mai suna Aquarius ya tsaya a gabar tekunta, Malta ta sauya matsayarta, bayan wasu kasashen nahiyar turai biyar da suka amince za su karbi bakin hauren.

Kasar ta Malta ta kwantanta wannan mataki da kasashen suka dauka, a matsayin manuniya ga irin shugabanci na-gari da kuma hadin kan kasashen nahiyar ta turai.

Daga cikin ‘yan gudun hijrar da kasashen na nahiyar turai za su karba, har da wadannan 141 da jirgin na Aquarius ya ceto, da kuma wasu 114 da kasar ta Malta ta ceto a tekun Meditareniya a ranar Litinin.

Sauran kasashen na nahiyar ta turai da suka amince za su karbi wasu daga cikin bakin hauren, sun hada da Jamus, Luxemburg, Portugal da Spain, yayin da sauran za su ci gaba da zama a kasar ta Malta.

Dubban mutane ne daga yankin kudu da hamadar sahara, da kasashen Syria da Afghanistan suke kokarin su bi ta kan tekun mediterranean duk shekara domin tserewa yake yake, da ta'addanci da talauci domin samun rayuwa mai inganci a turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG