Kasar Mexico ta bukaci Amurka a hukumance da ta yi cikakken bincike akan abinda ya faru ranar daya ga watan Janairu, lokacin da jami’an tsaron Amurka su ka harba barkonon tsohuwa, zuwa kasar Mexico domin hana bakin haure da suke kokarin shiga iyakar Amurka.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, Ma'aikatar Harkokin waje ta Mexico ta ce ba su yarda da duk wani cin zarafi da aka yi a bakin iyakar tasu ba, kuma ta na dada kira akan ayi bincike kamar yadda ya taba faruwa a ranar 24 ga Nuwamba.
A farkon shekarar nan ne, jami’an kula da iyaka na Amurka su ka harba barkonon tsohuwa zuwa iyakar Mexico, domin tsayar da bakin haure 150, wadanda suke kokarin shiga iyakar dake kusa da birnin San Diego dake Amurka.
A lokacin jami’an kula da iyaka sun ce bakin hauren sunyi kokarin haura katanga, ko kuma shiga ta karkashen katangar, amma jami’an sunyi amfani da barkonon tsohuwa ga wadanda suka jefo musu duwatsu.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum