Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Myanmar Ta Fara Maida 'Yan Gudun Hijirar Rohingya Gida


Shugaba Aung san suu kyi
Shugaba Aung san suu kyi

A wani al'amari da kasar Myanmar ta bayyana da shirin maido da 'yan gudun hijira gida, wanda kuma 'yan raji ke watsi da shi a matsayin bautar ganin ido, kasar ta Myanmar ta fara maida 'yan kabilar Rohingya gida.

Kasar Myanmar ta ce ta fara maido da ‘yan kabilar Rohingya masu gudun hijira zuwa gida.

To saidai kungiyoyin kare hakkin dana dam sun ce wannan ba wani abu ba ne illa na ganin ido saboda ba a dau matakan tabbatar da tsaron ‘yan Rohingya din da ke dawowa ba.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira ta fadi jiya Jumma’a cewa “har yanzu yanayin da ake cike a Myanmar inganta ta yadda zai kare lafiya da mutuncin ‘yan gudun hijirar da ke dawowa ba. Kuma hakkin tabbatar da wannan yanayin da ake bukata ya rataya a wuyar hukumomin Myanmar, kuma ya kamata hakan ya zarce batun tsare-tsare na ganin ido kawai ya kamata ya hada da batun zamantakewa da sauran tsare-tsaren rayuwa.

Kasar ta Myanmar ta fadi a wata takardar bayani cewa tuni wasu iyalai biyar su ka kammala shirin dawowa gida kuma har sun je wajen wasu ‘yan uwansu da ke garin Maungdaw, inda su ke jira na wuccin gadi a wannan wurin da ke daura da kan iyakar Myanmar din da Bangladesh.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG