Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Myanmar Ta Zargi Kasar Bangladesh da Kawo Cikas a Shirin Tsugunar da 'Yan Rohingya Musulmai


'Yan Rohingya dake ficewa daga Myanmar suna kan hanyar zuwa kasar Bangladesh
'Yan Rohingya dake ficewa daga Myanmar suna kan hanyar zuwa kasar Bangladesh

Kakakin shugabar kasar Myanmar ya shaidawa manema labarai cewa kasar Bangladesh na jiran karbar dalar Amurka miliyan dari hudu ne, kafin ta bar 'yan Rohingya 600,000 da yanzu suke makale a karamin wuri wucewa shiga kasarta

Kasar Myanmar na zargin makwabciyarta, Bangladesh, da kawo jinkiri ga dawowar Musulmin Rohingya, wadanda kuntatawar da sojojin kasar Myanmar ke masu ta tilasta masu gudu daga ksar.

Kakakin Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ya gaya ma kafar labaran gwamnatin Myanmar ta Global New Light of Myanmar jiya Laraba cewa da kasar ta Bangladesh ta na jira ne sai ta amshi dala miliyan dari hudu na fadada matsugunai ga ‘yan Rohingya 600,000 da ke cinkushe a matsattsun sansanonin da aka ajiye su.

Wani harin da mayakan Rohingya su ka kai kan ‘yansandan kasar Myanmar a watan Agusta, ne ya janyo ramuwar gayya daga jami’an tsaron gwamnatin Myanmar, wanda kuma ya janyo gudun hijirar ‘yan Rohingya da dama daga jahar Rakhine na arewacin kasar zuwa Bangladesh. Kusan kashi 60% na ‘yan gudun hijirar yara ne.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta bayyana yakin da jami’an tsaron gwamnati ke yi kan Musulmin Rohingya din da kisan kare dange.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG