Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Nijer Tace A Yi Koyi da Abunda Ya Faru a Burkina Faso


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Cikin firar da yayi da Muryar Amurka ministan harkokin wajem kasar Nijer Bazoum Muhammed yace wasu shugabannin kasashen Afirka dake shirin ta zarce yakamata abunda ya faru a Burkina Faso ya zama masu daratsi

Mr. Bazoum Muhammed yace a matsayinsu na shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ko CEDEAO ba zasu amincewa sojojin Burkina Faso su rike ragamar mulki ba. Dole su bar 'yan kasar su nada gwamnatin wucin gadi.

Ko menene ake son a yi lamarin yana hannun 'yan Burkina Faso. Su ne zasu zabi abun da suke so ba wai a dora masu wani abu ba alatilas. Amma idan sojoji ne zasu dauki shugabanci kungiyoyin nan biyu na Afirka da Afirka ta Yamma zasu dauki matakan da suka dace. Ana iya dakatar da kasar daga kungiyoyin a matsayin ladabtarwa.

Tun farko shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Issac Yacoubu ya umurci kungiyoyin su dan dakata su ga abun da 'yan kasar zasu yi. Akan wannan furucin Bazoum Muhammed yace muddin soji ne kan gaba a shugabancin kasar na rikon kwarya ba zasu amince ba.

Yace dadewa akan mulki komin iyawar mutum karshenta bakin jini yake jawowa. Yace Blaise Campaore yayi kuskure da ya nemi ya zarce bayan yayi shekaru 27 yana mulki.

Blaise Campaore shekaru uku da suka wuce shi ya umurci Tanja shugaban kasar Nijer na wancan lokacin ya manta da shirin ta zarce. Amma wai yau sai gashi yayi yunkurin yin abun da ya gayawa Tanja kada yayi. Yace yakamata wannan ya zama daratsi ga duk masu tunanen yin irin hakan.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG