Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Pakistan Ta Ce Za Ta Fara Samar Da Maganin COVID-19 Ga Duniya


Firaminista Imran Khan
Firaminista Imran Khan

Jiya Jumma’a kasar Pakistan ta ce cikin ‘yan makonni kawai za ta fara samar da maganin remdesivir don maganin COVID-19, wato cutar numfashi da coronavirus ke haddasawa.

Annobar ta hallaka mutane sama da 304,000 baya ga wasu kuma wajen miliyan 4.5 a sassan duniya tun bayan da cutar ta fara addabar China a watan Disamba.

Zafar Mirza, Ministan Lafiyar kasar Pakistan ya gaya ma manema labarai a birnin Islamabad cewa wani kamfanin harhada magungunan kasar mai suna Ferozons Laboratories Ltd, zai samar da maganin tare da hadin gwiwar kamfanin Gilead na Amurka, wanda ke yin remdesivir.

Ya bayyana cewa Pakistan za ta zama daya daga cikin kasashen nan uku da za su kirkiro tare da wanzar da maganin COVID-19 a duniya.

“Za a fara kirkiro maganin da ake allurarsa din ne cikin makonni shida zuwa mako 8 kuma zai samu ba ma kawai ga masu fama da coronavirus a kasar Pakistan ba, za kuma a samar da shi ga kasashe 127,” a cewar Mirza.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG