Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Ta Kara Lalata Dangantakar Diflomasiyarta Da Amurka


Russia
Russia

A jiya Laraba Rasha ta dakatar da yarjejeniyar shekaru uku da ta kulla da Amurka a kan makamashin nukiliya da nazarin harkokin makamashi, abinda ake ganin kamar wani mataki ne da zai kara lalata dangatakar diplomasiya a tsakanin kasashen biyu.

Daman tun ranar Litinin din da ta wuce Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu a kan dakatarda da wata yarjejeniyar ta daban da ta shafi kawarda ma’adinin “plutonium” a bisa hujjar cewa Amurka na daukar wasu matakai da “ban a abokanatka” ba – wanda ake ganin kamar arashi ne akan takunkumi da Amurkan ta kakabawa Rasha saboda take-taken ita Rasha din a kasar Ukraine.

Amurka ta dakatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da Rasha da ta shafi kasar Syria, a sabili da hare-haren jiragen sama da ake ci gaba da kaiwa a yankunan fararen hula na Syria din, abinda yassa Amurka take bayyana cewa hakurinta a kan Rasha ya zo karshe. To amma duk da haka jiya Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen Rasha Sergi Lavrov sun zanta da junansu a kan lamarin na Syria.

XS
SM
MD
LG