Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Babbar Barazana Ce Ga Amurka


Dan Coats
Dan Coats

Mutumin da shugaba Donald Trump ya zaba ya zama shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa ya bayyana Rasha a matsayin babbar barazana ga Amurka.

A jiya talata wannan dan talikin ya shaidawa ‘yan majilisar dokokin na Amurka cewa ba boyayyen batu bane cewa Rashar tayi yunkurin ganin tayi tasiri a zaben watan Nuwamba da aka yi.

Tsohon Sanatan Indiana, Dan Coats ya fada wa kwamitin bayanan sirri na tsaron kasa na majilisar dattijai cewa, da alamar Rasha ta nace wajen kumbiya-kumbiyrta don yin tasiri a zaben Amurka.

Akan haka ne yayi alkawarin cewa zai bada goyon bayan da duk ya dace domin ganin anyi binciken kwakwaf game da rawar da Rashar ta taka cikin wannan zaben na Amurka.

Ya ce, ba shakka wannan abu ne dake bukatar binciken kwakwaf domin fidda sakamako.

Coats dan shekaru 73 da haihuwa, kuma dan jammiyyar Republic, ya yi wannan kalamin ne sa’ilin da yake gaban majilisar dattijan domin a tantance shi game da wannan mukamin da shugaba Trump ya zabe shi ya rike.

Yaci gaba cewa ‘’Ina tsammanin duniya ta gama sani, kuma kowa ya yi amanna cewa ba shakka Rasha tayi yunkurin ganin tayi kutse cikin harkar kanfe, to sai dai ko tayi nasara ko kuma a’a, wannan shine bamu sani ba.’’

Sai dai kuma wannan matsaya da Coats ya dauka ba shakka za ta sa su samu rashin jittuwa da Donald Trump, wanda da farko ya wancakalar da binciken kwamitin tsaron wanda suka gudanar da farko, alokacin kanfe da kuma bayan kanfe. Domin ko rahoton farko da ofishin tsaron ya bayar daf da za a rantsar da Trump din ya nuna cewa Rasha tayi kutse a cikin wannan zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG