Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Na Dada Wargaza Libiya Don Ta samu Kafa Sansaninta a Ciki


Kasar Rasha na dada wargaza kasar Libiya saboda ta samu damar kafa sansanin saka ido kan arewacin Afurka, kamar yadda ta ke da shi a gabashin Turai da Gabas Ta Tsakiya, a cewar wani babban jami’i a Rundunar Sojin Amurka da ke Afurka (AFRICOM, a takaice).

“Kasar ta Rasha ta na amfani ne da irin dabarar nan da ta yi amfani da ita a Crimea, da Ukraine da kuma kasar Siriya. A baya Rasha ta nuna karara cewa a shirye ta ke ta wofinta diyaucin kasashe, kuma ga dukkan alamu ta yi harmar yin haka a Afurka,” abin da Burgediya Janar Gregory Hadfield, mataimakin daraktan sashin bayanan sirri na Rundunar ta AFRICOM, ya gaya ma manema labarai jiya Jumma’a kenan.

Hadfield ya ce sojojin Rasha sun kai jiragen yaki samfurin jet MiG-29 akalla guda 14 da kuma jirgi mai ruwan bama-bamai samfurin Su-24 cikin kasar kasar Libiya, tawajen rabewa da Iran da Siriya don su mara baya ga sojojin hayar da ke aiki ma Rashar wajen taya takarun da ke yaki da gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita. Ya ce sojojin Amurka su na kuma sane da wasu karin jiragen dakon kaya da su ka shigo cikin Libiya, da kuma wasu makaman linzami da su ka dan kwana biyu.

Tun da farko a wannan satin, rundunar ta AFRICOM ta fitar da wasu hotunan jiragen Rasha samfurin MiG-29 a sansanin al-Jufra da ke kasar ta Libiya wadanda ta ce an sake masu fenti ne a kasar Siriya saboda a boye asalinsu na Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG