Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Saudiya Zata Kulle Hanyoyin Shiga Yemen


Rundunar hadin gwiwa da kasar Saudiyya ke jagoranta dake yaki da masu tada kayar baya na kungiyar Houthi a Yemen ta ce zata kulle hanyoyin shiga Yemen ta kasa da ruwa da kuma filayen sauka da tashin jiragen sama na wani dan lokaci

Rundunar hadin gwiwa da kasar Saudiyya ke jagoranta wadda ke yaki da masu tada kayar baya na kungiyar Houthi a Yemen ta ce zata kulle hanyoyin shiga Yemen ta kasa da ruwa da kuma filayen sauka da tashin jiragen na wani dan lokaci, yayin da take zargin kasar Iran da hannu wajan kai harin makami mai linzami a Riyadh.

Rahotannin hadin gwiwa da kafar sadarwar gwamnatin Saudiyya ta fitar yau litini, sun bayyana cewa za a rufe iyakokinne domin inganta sababbin matakan da aka dauka na sa ido domin gano yadda makamai masu linzami da sauran kayan soji ke kai hannun kungiyar Houthi, amma za a kula da yadda kungiyoyin da ke kai taimakon daukin gaggawa zai su iya shiga.

Kasar Saudiyya da jima tana zargin kasar Iran da taimakawa masu tada kayar baya yaki da halartacciyar gwamnati, kasar Iran ta musanta zargin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG