Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Somalia Ce Ta Fi Yawan Kashe 'Yan Jarida a Duniya


Jana'izar wasu 'yan jarida da aka kashe, Mohamed Abdikarim Moallim Adam, da Abdihakin Mohamed Omar,
Jana'izar wasu 'yan jarida da aka kashe, Mohamed Abdikarim Moallim Adam, da Abdihakin Mohamed Omar,

Kwamitin 'yan jarida na kasa da kasa ya ce ko a wannan shekarar ma kamar shekaru biyun da suka gabata, kasar Somalia ce ta fi kowace kasa kashe 'yan jarida ba tare da gano wadanda suka kashesu ba

Kwamitin Kare ‘Yan Jarida na Kasa-da-Kasa, ya ce a jere a kuma karo na uku Somalia, ita ce kasar da ta fi yawan matsalar kashe ‘yan jarida ba tare da an gano wadanda suka yi kisan ba.

A kiddidigar da ya yi a karo na goma, wanda aka fitar a jiya Talata, kwamitin ya ce sama da dozin biyu na ‘yan jarida aka kashe cikin shekaru goma da suka gabata a Somalia, wacce ke fama da dadden yakin basasa.

Syria wacce ta kwashe shekaru shida ita ma tana fama da yakin basasa, ta zo ta biyu a matsayin kasar da aka fi kashe ‘yan jarida, bayan da ta dauki matsayi na uku a kididdigar bara.

Iraqi ita ce kasa ta uku da aka fi kai hari akan ‘yan jarida, inda kungiyar IS da sauran mayakan sa-kai da ke samun goyon bayan gwamnati ke kai masu hari.

Rikicin siyasar da ake fama da shi a Sudan ta Kudu, inda aka kashe ‘yan jarida biyar a wani harin kwantan bauna a shekarar 2015, ya kai kasar samun matsayi na hudu a kididdigar.

Kasar Philippines kuma ita ce ta biyar, inda jami’an gwamnati da masu aikata muggan laifuka sukan kade rigarsu su tafi ba tare da an hukunta su ba, idan sun kashe ‘yan jarida da dama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG