Saudiyya ta ce kasar Iran tayi abinda ta kira “takalar yaki” lokacin da ‘yan tawayen Houthi da Iran din ke marawa baya a Yamal suka harba makami mai linzami akan birnin Riyadh.
Saudi dai ta tare makami mai linzamin da aka harba filin jiragen saman King Khalid ranar Asabar.
Sojojin kawance na hadin gwiwa dake yakar ‘yan Houthi da Saudi ke jagoranta, ta ce tana da ikon mayar da martanin soja kan abin da Iran ta yi.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir, ya fada a shafinsa na Twitter cewa “katsalandan din da Iran take a yankin, na kawo barazana ga makwaptan kasashe, yana kuma shafar zaman lafiya da tsaro.”
Iran ta musanta cewa tana baiwa ‘yan tawayen Houthi makamai, kuma ministan harkokin wajen Iran din Mohammed Javad Zarif ya caccaki Saudiyya, kan zama sanadiyar asarar rayuka da rasahin zaman lafiya a Yamal.
Facebook Forum