Accessibility links

Kasashe Masu Harshen Faransanci Sun Rungumi Shirin Takaita Haifuwa


Shugaba Mouhammadou Issouffou, Junhuriyar Nijer

Burin shirin da USAID ta kaddamar shi ne a samu mata su takaita haifuwa nan da shekarar 2015 a cikin kasashe biyar na Afirka.

Hukumar tallafawa kasashe domin cigaba ko USAID a takaice ta kaddamar da shirin tallafawa mata a kasashe biyar dake anfani da harshen Faransanci su tsagaita haifuwa nan da shekarar 2015

Kasashen da suka taru a Jamhuriyar Niger sun hada da Mauritania da Togo da Burkina Faso da Ivory Coast da mai masaukin baki Niger. Hukumar USAID da hukumomin tallafawa iyali na kasashen biyar suka kaddamar da wannan tsarin a Niamey.

Ana zaton sama da kashi 50 na matan kasashen biyar zasu yi anfani da magungunan tsagaita haifuwa kafin shekarar 2015. Madam Maichibi Khadijatu Dandobi ministar mata da kyautatawa al'umma a jamhuriyar Niger ta ce rashin hutu shi ke kawo matsala da yawa.Misali mace ta dauki cikin wata tara bayan ta haifu zata bada nono amma tun kafin yaro ya yi karfi ta dauki wani cikin, irin wannan ke kawo matsala ga mace.Ta ce abun da ya fi dacewa shi ne a ba yaro nono har shekara biyu kafin a yi wani cikin. Yayin da ta sake haifuwa yaron farko ya kai shekara uku, ya yi wayo, kuma zai iya sani lokacin da ya ji kishirwa.

Masana daga wadannan kasashen sun kwatanta irin mace-macen da ake samu na mata a wurin haifuwa da yara kanana nada nasaba da rashin saka tsarin inganta iyali. Daraktan kula da fanin kiwon lafiya ta USAID ta ce ba shakka saka tsari a sha'anin haifuwa na kara tattalin arzikin iyali. Ta ce duk lokacin da iyali suka kyautata tsarin haifuwa suna kara harzukawa tare da kara tallafawa wajen magance matsalolin yau da kullum da ake samu. Kana hakan zai kara habbaka tattalin arzikin iyali da na kasa.

A janhuriyar Niger shirin zai yi aiki a Maradi da Niamey da wasu garuruwa. Shirin zai yi aiki da mata da sarakunan gargajiya da kungiyoyi. Tsarin zai share wajen shekaru biyar ana gudanar da shi daga shekararun 2012 zuwa 2018 kuma zai lakume dalar Amurka miliyan 25.

Ga rahoto.

XS
SM
MD
LG