Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Matalauta Da Masu Tasowa Su Na Hasarar Dala Miliyan Dubu 450 Kowace Shekara A Dalilin Yunwa


Kungiyar ActionAid ta ce su na hasarar wannan kudi ne wajen kula da lafiya da kuma rashin iya zuwa aiki na masu fama da yunwar

Wata kungiyar yaki da talauci mai hedkwata a kasar Afirka ta Kudu ta ce yunwa tana sanya kasashe matalauta da masu tasowa su na yin hasarar dala miliyan dubu 450 a kowace shekara wajen kula da lafiya da kuma rashin iya zuwa aiki na masu fama da yunwar.

Wannan sabon rahoto na Kungiyar ActionAid ya nazarci yunkurin yaki da yunwa a kasashe 28 masu tasowa. Ta ce kasashe 20 daga cikin 28 da ta nazarta ba zasu iya cimma gurin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a 2000 na rage yawan masu fama da yunwa da rabi nan da shekarar 2015 ba.

Rahoton yace kasashen da suke kashin baya a kokarin rage yunwa sune Lesotho da Pakistan da Saliyo da Burundi da kuma Kwango ta Kinshasa.

Kasashen da suke sama a kokarin yakar yunwa sune Brazil da China da Ghana da Malawi da kuma Vietnam. Kungiyar ActionAid ta ce wadannan kasashe biyar sun tashi haikan wajen zuba jari a kananan gonaki da shirye-shirye kamar samar da ayyukan yi na gwamnati da kuma ba ‘yan makaranta abincin rana kyauta a makarantunsu.

Har ila yau kuma, ActionAid ta auna kokarin kasashe masu arziki su 23 wajen tallafawa yaki da yunwa a duniya. Ta ce kasashen da suka fi taimakawa su ne Luxembourg da Faransa da Spain da Sweden da kuma Canada. Kasashe masu arziki dake baya a kokarin tallafawa yaki da yunwa sune Austria da New Zealand da Greece da Koriya ta Kudu da kuma Portugal.

XS
SM
MD
LG