Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mauritania sun kai farmaki kan ‘yan kungiyar al-Qaida da suke garkuwa da wasu mutane bakwai


Dakarun Mauritania sun kai faramaki kan reshen kungiyar al-Qaida na Afrika a Mali yau asabar, sai dai babu tabbacin ko farmakin da aka kai yana da alaka da garkuwa da ‘yan kasar Faranshi biyar da kuma wasu ‘yan afrika biyu da aka yi a jamhuriyar Niger.

Dakarun Mauritania sun yi arangama da reshen kungiyar al-Qaida na Afrika a Mali yau asabar, sai dai babu tabbacin ko sumamen da aka kai yana da alaka da garkuwa da ‘yan kasar Faranshi biyar da kuma wasu ‘yan afrika biyu da aka yi a jamhuriyar Niger. Babu cikakken bayani dangane da bata kashin da aka yi yau asabar. Jami’an kasar Faransa sun hakikanta cewa reshen kungiyar al-Qaidan na arewacin afrika ya sace mutanen ranar alhamis da safe duk da yake babu kungiyar da ta dauki alhaki. Jami’an tsaro sun ce an hango mutanen takwas da ake garkuwa da su a garin Arlit dake arewacin Niger jiya jumma’a suna ketare kan iyaka zuwa kasar Mali tare da wadanda suka sace su. Mutanen da ake garkuwa da su sun hada da wani mutum dake aiki da kamfanin nukiliya na kasar Faransa da matarsa, da kuma wasu kananan ‘yan kwangilar kamfanin biyar. Hukumomi na kira ga duk ‘yan asalin kasar Faransa dake aiki a yankin su fice daga garin.

XS
SM
MD
LG