Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Sun Shirya Tsaf Don Fito Da Tsarin Bai Daya Na Yaki Da Ta’addanci - Ministan Tsaro


Tawaga a taron yaki da ta'addanci
Tawaga a taron yaki da ta'addanci

Jim kadan bayan kamalla wani babban taro na musamman a kan yaki da ayyukan ta’adanci a nahiyar Afrika, kasashen nahiyar baki daya sun ce sun shirya tsaf don fitar da sabbin dabarun bai daya na yaki da matsalolin tsaro a matakin shiyya, tare da goyon bayan wasu kungiyoyin kasashen Turai kamar EU.

An cimma wannan matsayar ne a karshen taron yini biyu na yaki da matsaloli masu alaka da ta’addanci a nahiyar Afrika da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da goyon bayan ofishin kula da ayyukan ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya.

Babban ministan tsaron Najeriya, Mallam Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa taron ya cimma matsayar fitar da dabarun bai daya na nahiyar Afrika wajen yaki da ayyukan ta’addanci kuma kasashen sun shirya don daukar matakai na gaba, wadanda nan bada jimawa ba za’a fara fitar da su.

Minista Badaru Abubakar
Minista Badaru Abubakar

Wakiliyar mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Turai mai kula da yankin Sahel Emanuela C Del Re, ta ce ganin irin kokarin da Najeriya ta yi wajen hada kan dukkan kasashen nahiyar a wani kokari na kawo karshen ta’addanci a nahiyar ya sa kungiyar EU zata ci gaba da bada goyon baya a kokarin da ake yi, kuma akwai shirye-shiryen kungiyar da yawa da aka tsara da zasu taimaka.

Wakiliyar EU Emanuela C Del Re
Wakiliyar EU Emanuela C Del Re

A akasarin lokuta ana ganin rashin hadin kan masu ruwa da tsaki shi ne matsalar da ya kamata a tunkara kai tsaye, sai dai tsohon kwamishinan yada labarai kuma tsohon mamban kwamitin tsaro na jihar Adamawa, Mallam Ahmad Sajoh, ya ce an sami nasara a aikin hada kan dukkan masu ruwa da tsaki a fannin.

Masana dai sun ce idan ana son samun nasara a yaki da ta'addanci a nahiyar Afrika ya kamata masu ruwa da tsaki, da kungiyoyin yankunan nahiyar Afirka su taka muhimmiyar rawa wajen fitar da sabbin tsare tsaren bai daya na magance matsalar, wadanda zasu taimaka matuka wajen kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.

Saurari rahoton Halima Abdulrauf Muryar:

Kasashen Afirka Sun Shirya Tsaf Don Fito Da Tsarin Bai Daya Na Yaki Da Ta’addanci - Ministan Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG