Kasashen Australia da Singapore sun dakatar da amfani da jirgin sama kirar Boeing 737 Max 8 a duk ilahirin tashoshin kasashen, inda su ma suka shiga sahun sauran kasashe da suka dauki irin wannan matakin a matsayin rigakafi, tun bayan faduwar jirgin a karo na biyu a cikin watanni biyar.
Kasashen duniya da dama da suka hada da China, Indonesia, Brazil da Mexico duk sun dakatar da amfani da nau’in jirgin tun bayan mutuwar fasinjoji 157 a lokacin da jirgin 737 Max 8 na kasar Habasha ya fado a ranar Lahadi jim kadan bayan tashinsa sama daga filin jirgin Addis Ababa.
Sai dai sanarwar da kasashen Australia da Singapore, suka bayar tace dakatarwar ta wucin gadi ce, har sai an kammala binciken sanadiyar faduwar jigin na ranar Lahadi.
Jirgin sama na Habasha Max 8 kirar su daya da jirgin da ya fada cikin tekun Java a watan Oktobar bara, wanda ya fado jim kadan bayan tashin shi daga babban filin jirgin saman Jakarta, kuma hatsarin ya janyo mutuwar mutane 189.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 30, 2023
Kamala Harris Ta Gana Da Mata ‘Yan Kasuwa Na Kasar Ghana
-
Maris 29, 2023
Zimbabwe Na Duba Yiwuwar Soke Hukuncin Kisa
-
Maris 29, 2023
Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.
Facebook Forum