Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun Riga Sun Tserewa Na Afirka - Buhari


Shugaba Buhari yayinda yake jawabi a Majalisar Dinikn Duniya
Shugaba Buhari yayinda yake jawabi a Majalisar Dinikn Duniya

A jiya ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kammala ziyarar da ya kawo nan Amurka domin halartar taron koli na Majlisar Dinkin Duniya da ake yi inda aka yi muhawara akan dawwamammun Muradun Raya Kasashe 17 da aka tsara, wato Sustainable Development Goals SDG's a turance, domin kawar da matsalolin da suka shafi talauci da yunwa da kare muhalli da dai sauransu

Gabanin tahowarsa, abokin aikinmu Mahmud Lalo, ya zanta da shugaban na Najeriya,inda da farko ya tambayeshi ko kasashen Afrika za su iya cimma wadannan muradun da aka tsara guda 17. Sauran kasashen duniya na iya tserewa kasashen Afirka.

Sai shugaba Buhari yace ai an riga an tsere masu. Yace duk wanda ya fika ilimin zamani na kimiya, ya kafa ma'aikatu da yawa, ya samawa mutanesnsa aiki , yana noma abun da zai ci ba sai ya sayi abinci ba, ya tabbatar yana da kwararrun jami'an tsaro, yara na zuwa makaranta tare da basu lafiya ta zuwa asibiti, albashi yana zuwa kan kari, duk wadannan su ne zaman lafiya da wadata.

Akan rashin halartar taro akan yaki da Boko Haram duk da ikirarin da gwamnatinsa ke yi na yakar kungiyar shugaba Buhari yace sai mutum ya san da taron zai iya kasancewa wurin. Yace ba'a sanardasu batun taron ba.

Idan ana tababar matsayin gwamnatinsa kan yakar kungiyar Boko Haram shugaba Buhari yace yaya za'a yi haka. Cikin mako daya da rantsar dashi ya tafi Nijar da Chad duk akan batun yaki da Boko Haram. Da ya wuce zuwa Kamaru idan ba domin kiransa da aka yi a Jamus ba domin ya kasance wurin taron kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki da masana'antu a duniya. Amma da dawowarsa ya wuce Kamaru. Bayan Kamaru shugaba Buhari ya je Benin.

Banda ziyarar da ya kai kasashen nan na yammacin Afirka dake kewayen tafkin Chadi shugaba Buhari yace sun shirya taron hafsan hafsoshin sojojinsu kasa a Abuja. Bayan taron sojoji ministocin tsaron kasashen nan Benin, Kamaru, Nijar, Chadi da Najeriya sun hadu a Abuja. Suna gamawa shugabannin kasashen su ma suka yi taro a Abuja duk akan yaki da Boko Haram.

Shugaba Buhari yace duk tarukan domin yadda kasashen nan na kewayen tafkin Chadi zasu hada karfi da karfe su yaki Boko Haram ne.

Bisa ga furucin shugaban da majalisa ta soma zama zata sami sunayen wadanda zai nada ministoci.

Ga rahoton Mahmud Lalo.

Kasashen Duniya Sun Riga Sun Tserewa Na Afirka - Buhari - 4' 05"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG