Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen ECOWAS Basu Cika Alkawarin Sakarwa Mata Ragamar Samun Shugabanci Ba


Taron shugabannin ECOWAS

Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO na taron kwana biyar a Jamhuriyar Nijar da zummar lalubo bakin zaren yadda zasu cika alkawarin da suka yi na sakarwa mata ragamar shugabanci walau ta hanyar zabuka ko nade-nade

Sakar wa mata ragamar samun matsayin shugabanci ta hanyar zabe ko nade-nade na cikin alkawurran da Kungiyar Bunkasa tattalin Azriki ta Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, suka yi tun a shekarar 2015, amma har yanzu yawancinsu basu cika alkawarin ba.

Kan hakan ne, Kungiyar ta shirya taron duba matsalar a Junhuriyar Nijar domin binciken dalilin da ya sa aka samu tsaiko wajen cika alkawarin.

Sani Bukari, shugaban tawagar Nijar a wajen taron, yace gane cewa rayuwa sai da mata, shi yassa suka taron don a ga yadda za’a iya cika alkawarin da aka yiwa matan.

Ministar cigaban mata da bayar da kariya ga yara ta Nijar, Madam Zainabu Tari Bako, ta jinjinawa ECOWAS akan wannan yunkurin da tace yana da alfanu ga cigaban alumma.

Ga Souley Moumouni Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG