Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen G20 Sun Amince a Sauya Tsarin Karbar Kudaden Haraji

Lokacin da Sakataren baitulmalin Amurka Steven ya ke gabatar da jawabins a taron G20 a Japan
Lokacin da Sakataren baitulmalin Amurka Steven ya ke gabatar da jawabins a taron G20 a Japan

Shi dai taron, ya tattaro ministocin ne, da zimmar samar da sabbin tsare-tsare kan biyan kudaden haraji, wanda za’a auna kan yadda kamfani ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a wata kasa, bai inda hedkwatar kamfanin take ba.

Taron ministocin kudi na kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wato G20, wanda ke gudana a birnin Fukuoka a Japan, ya amince a yau Asabar cewa, akwai bukatar gaggawa ta tabbatar da cewa manyan kamfanoni suna biyan kason kudaden da ya kamata su biya.

Gangamin ministocin ya bayyana bukatar hakan ne yayin da aka fahimci cewa tattalin arzikin duniya, na tafiyar hawainiya wajen bunkasa.

Ministan kudi a Japan, Taro Aso, ya ce akwai bukatar a kaucewa yanayin da zai sa a samu wani fanni ya fadi warwas, saboda sauye-sauyen da za a yi, wadanda ya ce suna da muhimmancin da ba za a ga irinsa ba cikin karbi guda.

Shi dai taron, ya tattaro ministocin ne, da zimmar samar da sabbin tsare-tsare kan biyan kudaden haraji, wanda za’a auna kan yadda kamfani ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a wata kasa, bai inda hedkwatar kamfanin take ba.

A kuma cewar Sakataren baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin, bai kamata a rika nuna banbanci kan harkokin kasuwancin da ake yinsu a fili ba da wadanda ake yi a kafar yanar gizo.

Sai dai duk da cewa ministocin kasashen da suka ci gaba da wadanda ke kan bunkasa, sun yi hannun riga a wasu shawarwarin da aka gabatar a taron, taron ya amince cewa akwai bukatar a samar da sauye-sauye kan yadda ake karbar kudaden haraji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG