Shugabannin kasashen duniya da suka yi taron G7 a kasar Faransa, sun kuduri aniyyar samar da dala miliyan 22 a jiya Litinin, don yakar wutar dajin nan da ke ta ci a kasashen yankin kurmin nan na Amazon a nahiyar Kudancin Amurka, wadda ke barazana ga wannan jikakken kurmin dausayi mafi girma a duniya.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, wanda shi ne mai masaukin bakin taron, da Shugaban Chile, Sebastian Pinera, wanda ya kai ziyara wurin taron, sun ce jikakken kurmin wanda ke ta ci da wuta yanzu, kusan shi ne huhun duniya saboda aikin zukar dagwaluwar iskar Carbon dioxide da ya ke yi, ya na maye ta da iskar shaka ta oxygen.
Macron ya ce cikin ‘yan sa’o’i kasar Faransa za ta samar da sojojin da za su agaza a yankin, don yakar wannan wutar.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe
Facebook Forum