Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashedin Kotun Duniya na Iya Tasiri a Zaben Najeriya


Ginin Kotun Duniya
Ginin Kotun Duniya

Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya lura cewa Kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ka iya sa 'yan siyasa yin karatun ta natsu, ta wajen gargadi da kuma kashedin shirin daukar matakin da ya dace kan duk wani dan takarar da ya dayar da zaune tsaye.

Wani dan rajin kare hakkin dan adam kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum y ace akwai rawar da kotun duniya ta manyan laifuka za ta iya takawa kan zaben da za a yi a Nijeriya ganin yadda zaben ke tattare da sarkakiya da kuma yiwuwar a samu takaddama.

Da abokin aikinmu Bello Habib Galadanchi ya tambayi dan rajin mai suna Aminu Sule irin tasirin da ya ke ganin Kotun ta duniya ka iya yi game da zaben Nijeriya, sai Aminu Sule ya kara da cewa ganin ikon da kotun ke da shi, gargadin Kotun ka iya sa ‘yan siyasa su kai zuciya nesa su kuma bi al’amarin a hankali. Y ace lallai kashedin Kotun na iya sassauta duk wata tarzomar da ka iya aukuwa a gabani da kuma bayan zabe a Nijeriya. Da Bello ya tambaye shi matakan da Kotun ta dauka a baya, sai Aminu y ace Kotun ta sa an kama wasu an gurfanar da su a Kotu, sannan ta na kuma tuhumar wasu da laifuka.

Da aka tambaye shi abin da zai so gaya ma jama’a game da zaben sai y ace, ya kamata kowa ya yi kokarin ganin cewa an zauna lafiya lokacin zabe. Y ace su kuma hukumomin da abin ya shafa ya kamata su kamanta adalci a gabani da kuma bayan zaben don gudun tashin hankali da kuma tabbatar da adalci.

Kashedin Kotun Duniya na Iya Tasiri a Zaben Najeriya - 5'36"
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG