WASHINGTON, D.C —
Wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, ya yi hira da masu saye da sayarwa a kasuwar da kuma yanayin sana’ar baki daya.
Ayuba Auta, shi ne sarkin kasuwar doya ta garin Tagina, ya ce an sami ci gaba musamman ganin yadda doya ta yi daraja a bana kuma ana samun masu saye, duk da cewa farashinta ya hau.
Hakazalika wasu ‘yan kasuwar su ma sun shaida cewa an sami ci gaba a kasuwar, sai dai babbar matsalarsu ita ce rashin rumfuna.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments