Accessibility links

Kauracewa Kamfanonin Afrika Ta Kudu A Najeriya


Sumbatar Addar Saran Baki

Ana ta samun karuwar zanga-zanga a kasashen Afrika game da kashe-kashen bakin da 'yan Afrika ta Kudu ke yi a kasarsu inda mutane da dama suka rasa rayukansu. A jihar Legas ma Babangida Jibrin ya hada mana rahoton yadda abin ke tafiya.

Tun bayan hare-haren kin jinin bakin da ke wakana a Afrika ta Kudu ne ake samun karuwar zanga-zangar a wasu kasashen nahiyar Afrika don nuna rashin jin dadinsu game da kiyayyar ga baki.

A Najeriya ma an sami ire-iren wadannan zanga-zangar don kira da a gujewa amfanin da kayayyakin kamfanonin Afrika ta Kudu wajen nuna musu cewa da bazar 'yan Afrika suke rawa.

Sai dai wani manaja a kamfanin sadarwa na MTN mai suna Wale Goodluck yace idan har aka yi sanadiyyar rufe kamfanin to mutane ‘yan Najeriya sama da dubu shida za su rasa aikin yi.

Yace ba ma’aikatan MTN a Najeriya ba har ma da wasu mutane sama da dubu dari biyar masu cin abinci da kamfanin zasu rasa abincinsu. Ya kara da cewa ma’aikatan kamfanin da suke Najeriya bas u wuce guda goma sha biyar ba.

Wani mai suna Shola Akoka da ya taba zama a Afrika ta Kudu yace bay a goyon bayan kauracewa kamfanoninsu duk yasan cewa ‘yan Afrika ta Kudu basa mutunta baki kuma sun manta cewa ‘yan Afrika gaba daya ‘yan uwan juna ne. Ya dai kamata ayi abinda ya dace wajen shawo kan matsalar.

Shima Alhaji Garba Wazirin Sabo Yaba a Legas yace ya kamata kam mu nuna kishin mutanen Afrika da ake kashewa a Afrika ta Kudu ta hanyar kaurace wa kayayyakinsu.

‘Yan Afrika dai sun ji zafin wannan halayya ta Afrika ta Kudu ne saboda yadda sauran Afrikawa suka jajirce wajen tayasu fafutukar samun ‘yancin kai a lokacin da suke fama da mulkin mallaka.

XS
SM
MD
LG