Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kama Magajin Garin Nairobi a Kenya kan zargin cin hanci da rashawa


A tsakiyar wan nan hoto,shugaba Mwai Kibaki ne yake jawabi ga zaman majalisar dokokin kasar.

An kama Mr. Geophrey Majiwa,bisa zargin cin hanci da rashawa dangane da sayar da wani fili domin mayar da shi makabarta.

An kama magajin garin Nairobi kasar Kenya Geophrey Majiwa bisa caje cajen cin hanci da suka danganci sayar da wani filli domin maida shi makarbata.

A yau litinin jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar suka kama Mr Majiwa.

Hukumar tace Mr Majiwa da wasu jami’ai goma sha uku sun hada baki suka saci kimamin dala miliyan uku da rabi daga asusun ma’aikatar kanana hukumomi ta hanyar yin zambar kwangilan sayen wani filli.

XS
SM
MD
LG