Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Ce A Kai Kasuwa


Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, yana sauraren ministan harkokin wajen Qatar, Sheik Hamad Bin Jassem, (dama) da sakatare-janar na Kungiyar Kasashen Larabawa, Amr Moussa (hagu) a wani taro a Sirte, kasar Libya ranar Lahadi, 10 Oktoba 2010

Isra'ila ta ce zata jingine gina gidajen yahudawa a yankunan da ta mamaye idan Falasdinawa suka amince da Isra'ila a zaman kasar yahudawa.

Jami'an Falasdinawa sun sanya kafa suka yi fatali da tayin da Isra'ila ta yi musu jiya litinin, cewa zata sabunta dakatar da gine-ginen gidajen yahudawa a yankin yammacin kogin Jordan na wani lokaci idan har za su amince da kasar ta Isra'ila a zaman ta Yahudawa.

Firayim ministan bani Isra'ila, Benjamin Netanyahu, shi ne yayi wannan tayin jiya litinin a gaban majalisar dokokin kasarsa, inda yace amincewar zata sa Isra'ila ta sake yin amanna da Falasdinawa.

Amma shugabannin Falasdinawa suka ce batun kasancewa ko rashin kasancewar Isra'ila kasar Yahudawa, ba shi ne muhimmi a batun dakatar da gine-ginen a yankunan da Isra'ila ta mamaye ba. Falasdinawa su na son Isra'ila ta dakatar da ayyukan gine-ginen ta komo kan teburin shwarwarin neman zaman lafiyar da aka dakatar a wannan wata dangane da wannan batun.

Wannan fatali da Falasdinawa suka yi da tayin Mr. Netanyahu ya biyo bayan amincewar da majalisar ministocin Isra'ila ta yi da wani kuduri wanda zai bukaci duk wani mutumin da ba Bayahude ba dake neman zamowa dan kasa a Isra'ila ya yi alkawarin yin biyayya ga kasar Isra'ila a zaman kasar Yahudu mai bin tafarkin dimokuradiyya.

Larabawa 'yan majalisar dokokin Isra'ila da wasu a cikin kasar sun fito da kakkausar harshe su na yin tur da wannan kuduri wanda har yanzu majalisar dokokin Isra'ila ba ta amince da shi ba.

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Sham shi ma ya bayyana wannan mataki na Isra'ila a zaman na kama-karya da kuma nuna wariya.

XS
SM
MD
LG