Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muammar Gaddafi Yace Kuri'ar Raba-Gardamar Da Ake Shirin Yi A Sudan Cuta Ce Ga Illahirin Afirka


Wasu shugabannin Afirka da na larabawa a taron kolin kasashen Larabawa da na Afirka, lahadi 10 Oktoba, 2010 a birnin Sirte a kasar Libya

Shugaban na Libya ya fadawa taron kolin kasashen larabawa da na Afirlka cewa kuri'ar tana iya haddasa rarrabuwar kasashen Afirka da dama

Shugaba Muammar Gaddafi na Libya yace rabuwar kasar Sudan gida biyu tana iya haddasa wannan rarrabuwa a wasu kasashen larabawa da na Afirka. A lokacin da yake jawabi ga taron kolin shugabannin kasashen larabawa da na Afirka jiya lahadi, shugaba Gaddafi yace kuri’ar raba-gardama da za a yi kan ‘yancin kudancin Sudan a watan Janairu, mataki ne mai hatsari.

Gaddafi yace abinda ke faruwa a Sudan cuta ce, wadda zata yi illa ga dukkan Afirka, a saboda a karon farko tun bayan karshen mulkin mallaka, zata haddasa sake zana bakin iyakokin da Afirka ta gada daga turawa. Yace wannan na iya kawo rarrabuwar kasashe da dama a Afirka.

Shugaba Hosni Mubarak na Masar, kasar da ta fara karbar bakuncin taron kolin shugabannin Afirka da na larabawa a 1977, yace lokaci yayi na maida dangantakar kasashen ta zamo cikakken hadin kai, inda yace, "kashi 70 cikin 100 na kasashen larabawa su na nahiyar Afirka ne, yayin da kashi 20 cikin 100 na nahiyar Afirka larabawa ne. A saboda haka, lokaci yayi na maida irin wannan dangantaka ta zamo hadin kan ‘yan’uwantaka a inuwar Tarayyar Afirka da Kungiyar kasashen Larabawa."

Shugabannin Afirka da dama sun tabo batutuwan tattalin arziki da na siyasa da tsaro. Shugaba Idris Deby na kasar Chadi, yayi magana kan wata mummunar barazanar dake fuskantar kasashen Afirka da na larabawa, watau kwararowar hamada, yana mai cewa, "kwararowar hamada, da cikewa tare da konewar tabkuna da koguna, kamar kogin Naija ko Kwara, abubuwa ne da ya kamata kasashen Afirka su rungumi matakan dakile su, kuma matsaloli ne na yanki wadanda ya kamata a hadu a yi taron dangi wajen magance su."

XS
SM
MD
LG