Accessibility links

Kenya Ta Nemi Amurka Ta Taimaka A Kwace Kismayo

  • Halima Djimrao-Kane

Sojojin Kenya da na Somaliya a garin Tabda, kasar Somaliya

Firai Ministan kasar Kenya, Raila Odinga, ya ce burin su shi ne su shiga Kismayo nan da watan Agusta

Gwamnatin kasar Kenya ta bukaci Amurka ta taimaka da kudaden gudanar da wani samamen sojin da za a shirya da nufin kwace wata muhimmiyar tashar jiragen ruwa daga hannun mayakan al-Shabab.

A yau Talata Firai Minista Raila Odinga ya shaidawa manema labarai a birnin Nairobi cewa rundunar sojojin kasar Kenya na fatan kama garin Kismayo nan da watan Agusta.

Firai Minista Raila Odinga ya ce ”Burin mu shi ne mu shiga Kismayo nan da watan Agusta saboda tashar jiragen ruwan Kismayo ce babbar hanyar samar da kayan buk’atu ga al-Shabab, ganin bayan al-Shabab baki daya, zai yi wuya ba tare da kwace garin Kismayo daga hannun su ba”. Inji firai ministan kasar Kenya Raila Odinga.

Haka kuma Kenya ta bukaci taimakon mayakan ruwan Tarayyar Turai masu kula da fashin jiragen ruwan da ake yi a gabar tekun Somaliya.

Yanzu haka sojojin Kenya da Ethiopia da Somaliya da kuma na Kungiyar Kasashen Afirka ne su ka yiwa mayakan al-Shabab taron dangi, su na fafatawa da su har cikin kasar Somaliya.

Mr.Odinga ya bayyana cewa samamen da sojojin kasar Kenyar ke shirin kaiwa shi ne harin karshen da zai kai ga kwace Kismayo, daya daga cikin ‘yan wurare k’alilan da su ka rage a hannun mayakan al-Shabab.

XS
SM
MD
LG