Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya Zata Rufe Sansanonin 'Yan Gudun Hijira Biyu Da Suke Kasar.


Hoton sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya da ake kira Dadaab, dake arewa maso gabashin kenya.
Hoton sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya da ake kira Dadaab, dake arewa maso gabashin kenya.

Gwamnati kasar ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa mai shafi biyu data fitar ranar jumma'a.

A kenya gwanati tace tana shirin zata rufe manyan sansanonin 'yan gudun hijira biyu da suke kasar, mataki da zai shafi 'yan gudun hijira kimanin dubu dari hudu.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar jiya jumma'a, tace saboda dalilan tsaro, ta "yanke shawara cewa tilas a kawo karshen karbar 'yan gudun hijira."

Abunda kadai sanarwar mai shafi biyu bata yi ba shine ta fito ta ce ta kori 'yan gudun hijiran. Duk da haka tace gwamnati ta rusa ma'aikatar kla da 'yan gudun hijira, a zaman matakin farko, kuma tana aiki kan shirye shiryen rufe sansanonin da ake kira Dadaab, da kuma Kakuma, "cikin dan gajeren lokaci."

Sansanin Dadaab, dake arewacin kenya, shine sansani da ake kallo a zaman mafi girma a duk fadin duniya, inda ahalin yanzu akwai mutane 330,000, galibinsu 'yan kasar Somalia.Sannan sansanin Kakuma dake arewa maso yammacin kasar, akwai mutane dubu 55.

Kungiyar kare hakkin Bil'Adama ta Amnesty international, ta kira wannan shawara a zaman "ganganci" mataki da zai jefa dubban rayukan mutane wadanda basu aikata laifin komi cikin hadari. Wanda hakan zai tilastawa dubban 'yan gudun hijira komawa kasarsu ta asali watau, Somaliya, inda basu da tabbas kan rayukansu.

XS
SM
MD
LG