Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenyatta Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli


Shugaba Kenyatta yana magana a wannan hoton da aka dauka a talbijin kan soke zaben kasar da kotun koli ta yi a ranar 1 ga watan Janairu, 2017
Shugaba Kenyatta yana magana a wannan hoton da aka dauka a talbijin kan soke zaben kasar da kotun koli ta yi a ranar 1 ga watan Janairu, 2017

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ya amince da matsayar da kotun kolin kasar ta dauka na soke nasarar zaben shugaban kasar da ya lashe, amma kuma ya ce wannan matsaya ta tauye hakkin al'umar kasar da suka zabe shi.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce zai bi umurnin kotun kolin kasar, wacce ta soke nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya gabata, duk da cewa shi a gashin kansa ya ce bai amince da matsayar kotun ba.

Koda yake Kenyatta ya ce zai yi biyayya ga umurnin kotun, amma kuma bai nesanta kansa da caccakarta ba, inda ya ce “mutane shida sun yanke shawarar yin watsi da zabin jama’ar kasar.”

Kotun kolin kasar ta soke zaben ne saboda a cewarta, an “tafka magudi” a wajen jefa kuri’u, wanda ta ce hakan ya raunana sahihancin zaben.

Shugaban ‘yan adawa, Raila Odinga ne ya kalubalanci zaben a watan Agusta, yana mai cewa kuri’u miliyan 1.4 da Keynatta ya samu na bogi ne.

A ka’idar kundin tsarin mulkin kasar ta Kenya, dole ne a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Tun a ranar zabe, gamayyar jam’iyun adawan kasar da ake kira NASA a takaice, ta yi ikrarin cewa an kitsa tafka magudi a zaben ta hanyar yin kutse, wanda hakan zai ba da damar yin arangizon kuri’u.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG