Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kerry Yayi Tur Da Matakin Da Trump Ya Dauka Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran.


Donald Trump da John Kerry

Ranar jumma'a Trump ya birgita yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla na dakatar da shirin Nukiliyar Farisar.

Jiya jumma'a shugaban Amurka Donald Trump yayi amfani da kakkausar lafazi wajen ayyana cewa Iran bata mutunta yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Farisa kan shirin Nukiliyarta.

Mr. Trump ya kuma aza sabon takunkumi kan rundunar juyin juya hali na Iran dangane da ta'addanci.

Rahotanni suka ce kama-kafa da kawayen Amurka, dama wasu manya cikin gwamnatin ta Trump suka yi ne yasa shugaban bai yi fatali da yarjejeniyar ba baki daya.

Da yake magana kan wannan mataki, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John kerry da kakkausar lafazi ya soki matakin , yace wannan shawara "ganganci inda aka fi bada karfi kan izza da akida maimakon hujja ko shaida dake bayyane. Hakan inji Mr. Kerry ya gurgunta karfin Amurka, ya maida ita saniyar ware cikin kawayenta, ya kuma tsananta hanyoyin warware rikicin da ake yi da Koriya ta Arewa kan shirin Nukiliyarta, ya kuma kara tura Amurka zuwa ga shiga yaki."

Shima da yake magana a jiya jumma'an, shugaban Iran yace yarjejenyar d a Iran ta sanya hanu akai da kasashen duniya shida a shekara ta 2015, ba za'a iya warware shi ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG