Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiir Ya Gargadi Kabilun Joglein Da Pibor Su Daina Yaki Ko Kuma Ya Kyale Su Kashe Juna


Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Salva Kiir

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce gwamnatin sa ba zata kara jibge jami’an tsaro masu shiga tsakanin rikicin kabilanci idan yaki ya kaure a jihar Jonglei da garin Pibor na gwamnatin wurin, wani yanki da ake yawan samun mummunar arangama.

Ya ce “nan gaba idan kuka je kuka yi fada, ba zan kawo muku agaji ba kana ba zan kafa wani kwamiti da zai je inda aka yi yakin ba. Na yanke shawara duk wani rikici da zai sake tashi, ba zan aike da sojoji ko ‘yan sanda ba. zan kyale ku ci gaba da yaki har sai bangare daya ya gudu,” Salva Kiir ya fada a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a wani taron zaman lafiya tsakanin kabilun Jonglei da Pibor a birnin Juba.

Nan da nan masu sharhi a kan siyasa suka ce matakan da Kiir ke dauka a kan wannan batu basu dace ba, a dan haka sun kira shugaban kasar da ya janye wadannan kalamai nasa.

Augustino Ting Mayai, mai nazari da sharhi a cibiyar Sudd Institute, ya ce yana sa ran shugaban ya yi wadannan kalaman ne saboda ‘yan kasa na dubi ga gwamnatin kasar ta magance irin wadannan yake yake.

Mayai ya kyautata zaton al’ummomin ba zasu dauki kalaman shugaban a matsayin dalili da zai sa su ci gaba da kaiwa juna hari.

Sau tari ana samun yaki tsakanin kabilun ne sakamakon mamayan shanu da kuma satar kananan yara, kana ya kara ta’azzara da batu na kabilanci da kuma hare haren ramuwar gayya, lamarin dake kara zama babbar matsala a arewa maso gabashin Sudan ta Kudu.

Bayan wata arangama a wata Maris na bara, wata kungiyar taimakon kiwon lafiya ta Médecins Sans Frontières, ta ce ta yi jinyar mutum 45 da raunin harbin bindiga a Pibor kana sama da mutum 80 suka samu raunuka a Jonglei.

XS
SM
MD
LG