Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fari Ya Kashe Mafi Yawancin Dabbobi A Kasar Somaliland


Wani Mutum A Tsaye Gaban Kasusuwan Matattun Dabbobi A Somaliland

Fari ya hallaka dubban dabbobin 'yan karamar kasar nan ta Somaliland da ta balle ta ke zaman kanta. Mutane da yawa ma sai da wannan farin ya hallaka su kafin kaiwa ga dabbobin.

Jami’ai a karamar kasar nan ta Somaliland da ta balle daga cikin Somalia, sun ce kimanin kaso 80 cikin dari na Dabbobi a yankin sun mutu, sakamakon mummunan farin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Mohamud Ali Saleban, Gwamnan yankin Togdheer a garin Buro yace “Yanayin yayi tsanani sosai, akasarin Dabbobi duk sun mutu sakamakon Farin,”

Gwamnan ya fadawa VOA cewa “Muna jiran saukar ruwan sama, amma in bai sauka ba nan da makonni masu zuwa , muna sa ran gwamnati ta gabatar da yanayin gaggawa.”

Jami’ai sun fadawa VOA cewa kusan mutane 50 ne a fadin Somaliland suka mutu sakamakon farin da kuma cututtuka dake da dangantaka da farin.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG