Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane Ashiri ne Suka Nufi Gidan


Wata zabiya daga jihar Enugu

Mutane da aka kama dagane da zanga-zangar gidan gwamnatin jihar Enugu sun bada sunayen wadanda suka turo su.

Kimanin mutane ashirin ne zuka nufi gidan gwamnatin jihar Enugu da zanga-zanga ta kuma nufin kafa tutar neman kasar Biafra.

Jami'an tsaro dake kula da gidan gwamnati,sun tarwasasu, inda suka harbi mutun daya amma bai mutu ba da kuma kama hudu daga cikin su, inda aka karbe makamasu da kuma yan tsubace-tsubace da suka zo dashi.

Masu zanga- zangan dai daga jihar Anambra suka fito inji kwamishina yan sandan jihar Abubakar Adamu Muhammad a hira da suka yin da wakiln mu ta wayar tarho.

Kwamishinan yace a yanzu haka ana bin cikan mutane domin sanin gaskiya abinda ya kawo su, shin bayan neman kafa tuta, akwai wata manufa na daban,da kuma neman sanin wadanda suka turosu.

Yanzu haka su bada sunayen wasu daga cikin wadanda suka gayyato su inji kwamishina yan sandan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG