Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane Miliyan 40.3 Ke Aikin Bauta A Duniya


Wasu 'yan Afirka a yayin da suke wata zanga-zanga a Isra'ila.
Wasu 'yan Afirka a yayin da suke wata zanga-zanga a Isra'ila.

Sakamakon wani bincike da aka fitar, ya nuna cewar Korea ta Arewa da Eritrea, sune kasashen da aka fi samun matsalolin aikin bauta a duk fadin Duniya.

Binciken na alkaluman ayyukan bauta na shekarar 2016 da aka fitar jiya Alhamis, ya yi kiyasin cewa mutum miliyan 40.3 a duk fadin Duniya, na fuskantar wannan matsalar.


Binciken ya bayyana ayyukan bautar da mutane a zamanance a matsayin “safarar mutane, tilastawa mutane yin aiki, bautar da mutane saboda bashi, auren dole, da cinikin yara kanana da kuma shi kansa cinikin bayi.”


Rahoton ya nuna cewa, Korea ta Arewa ita ce kasar da aka fi samun wannan matsala ta bauta, inda mutum daya cikin kowanne kashin mutane goma ke fama da wani nau’in aikin bauta, yayin da “kasar ta ke tilastawa aksarin jama’arta yin aiki.”


Manufar fitar da wannan sakamakon bincike, shi ne a tilastwa gwamnatoci su kara himmatuwa wajen kawo karshen wannan matsala, saboda irin tasirin da hakan ke yi ga Duniya. Rahoton yana aibanata manyan kasashen duniya saboda sayen kayayyakin da aka sarrafa ta bautar da mutane.


Baya ga Korea ta Arewa da Eritrea, sauran kasashen da matsalar ta bauta ta yi kamari, sun hada da Burundi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Afghanistan da Mauritania, da Sudan ta Kudu da Cambodia da kuma Iran, a cewar rahoton.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG