Accessibility links

Kimanin Mutane Miliyan 7 Suke Samun Jinyar HIV A Afrika


Ana jinyar wata mai fama da cutar HIV

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa adadin wadanda suke shan maganin kashe kaifin Cutar kanjamau a kashen nahiyar Afirka ya karu daga miliyan daya zuwa kusan miliyan bakwau a cikin shekaru bakwai.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa adadin wadanda suke shan maganin kashe kaifin Cutar kanjamau a kashen nahiyar Afirka ya karu daga miliyan daya zuwa kusan miliyan bakwau a cikin shekaru bakwai.

Bisa ga rahoton, yawan masu shan maganin kashe kaifin cutar ya karu daga mutane miliyan daya a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar zuwa miliyan bakwai da dubu dari a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu. Aka kuma samu karin masu shan maganin kimanin miliyan daya a cikin shekarar da ta gabata.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana cewa, an sami raguwar mace-mace ta dalilin cututan da cutar kanjamau take sawa da kusan kashi talatin da biyu cikin dari daga shekara ta dubu biyu zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

An bayyana cewa an samu ci gaba a yaki da cutar ne saboda maida hankali da shugannin nahiyar da kuma sauran alummar kasa da suka yi. Rahoton ya kuma nuna cewa kashe goma sha shida na nahiyar Africa suna ba mata masu ciki maganin kashe kaifin cutar kanjamau domin kada jaririnsu su dauki cutar.
XS
SM
MD
LG