Accessibility links

Kimanin Mutane Milyan Dari Uku A Afirka Basa Samun Ruwan sha Mai Tsabta

  • Aliyu Imam

Kogi.

Masu ilimin kimiyya sun ce, kimanin mutane miliyan dari uku a Afrika basu samun ruwan sha mai tsabta, kuma lamarin nasu yana fuskantar karin barazana yayinda sauyin yanayi ya sa rashin tabbas a samun ruwan sama.

Masu ilimin kimiyya sun ce, kimanin mutane miliyan dari uku a Afrika basu samun ruwan sha mai tsabta, kuma lamarin nasu yana fuskantar karin barazana yayinda sauyin yanayi ya sa rashin tabbas a samun ruwan sama.

Sabili da haka nazari a kan makekiyar matattarar ruwa a karkashin kasa a nahiyar yake da ma’ana.

Richard Taylor wani masanin ruwa ne a Jami’ar birnin London yake cewa: abinda muke fadi a nan shine, akwai ruwa kwance karkashin kasa a Afrika da zai iya taimakawa wajen sa kasa ta kasance da laima da zai kai ga samar da isasshen abinci.

Binciken ya yi kiyasin cewa, akwai kimanin ruwa da yawansa ya kai fadin murabba’in kilomita digo dubu 660 kwance a karkashin kasa a nahiyar, wanda ya ninka ruwan da ake samu a kan doron kasa sau dari.

Taswirar da ma’aikatar kasa da safiyon kasar Birtaniya da kuma jami’ar birnin London suka samar, ta nuna ruwan dake karkashin kasa yafi yawa a kasashen Libya da Algeriya da Misira da kuma Sudan.

Binciken na nuni da cewa, yana yiwuwa kasashen da aka ayyana a halin yanzu a matsayin masu “karancin ruwa” suna zaune a kan makeken tabkin ruwan da zurfinsa bai wuce mita 10 sha wani abu daga kan doron kasa ba.

A halin yanzu, ana yin noman ban-ruwa a kashi 5 cikin 100 na gonakin nahiyar Afirka ne kawai. Masu ilimin kimiyya sun yi hasashen cewa, bukatar ruwa zata karu ainun tare da habakar al’umma.

Sai dai kuma, akwai fargabar jawo ruwan karkashin kasa fiye da kima. Amma kuma Taylor yace, za a kaucewa shiga wannan halin kasancewa manoman Afirka kanana ne.

Cibiyoyin agaji sun yi gargadi da cewa, akwai yiwuwar fuskantar karancin abinci a Niger, da kuma Mali. Taylor ya bayyana cewa, ba lallai ne haka rijiyoyin burtsatsai domin janyo ruwan dake karkashin kasar, ya shawo kan wadannan matsalolin shi kadansa ba.

Yace abinda yasa muke kiddiga, da kimanta albarkatun ruwan karkashin kasar dake wurare da dama shine, domin samo hanya mafi nagarta ta yin amfani da ruwan karkashin kasa a zaman daya daga cikin dabarun bunkasa noman abinci da shawo kan illar karancin ruwan sama.

Masanan da suka gudanar da wannan bincike, sun ce ba wai tabbas ruwan karkashin kasa dake kwance a nahiyar Afirka zai iya warware dukkan matsalolin ruwa da na abinci ba ne, amma yana iya samar da kafa mafi dogaro fiye da ruwan saman da samunsa a wadace babu tabbas.

XS
SM
MD
LG