Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristoci Da Masu Rajin Kare Hakki Sun Yi Zanga-Zanga A Pakistan


Kiristoci su na zanga-zanga a Pakistan

Masu zanga-zanga a Islamabad, sun soki gwamnati a saboda ta kasa kare ministan ‘yan tsiraru Shahbaz Bhatti, wanda aka harbe a kusa da gidansa

Kiristoci ‘yan tsiraru da ‘yan rajin kare hakkin bil Adama a Pakistan sun fito kan tituna domin zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe ministan gwamnati kwaya daya kirista da aka yi a bayan da ya kalubalanci dokar sabo ta kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Islamabad, inda aka kashe ministan ranar laraba, sun soki gwamnati a saboda ta kasa kare ministan ‘yan tsiraru Shahbaz Bhatti, wanda aka harbe a kusa da gidansa.

‘Yan majalisar dokoki daga bangaren ‘yan tsiraru na Pakistan sun fice lokacin wani zaman majalisa. Sun bukaci gwamnati da ta dauki duk matakin da zata iya domin hukumta wadanda suka yi kisan.

Firayim minista Yousuf raza Gilani, ya bayyana zaman makokin kwana uku domin jimamin dan siyasar da aka kashe, ya kuam lashi takobin murkushe ta’addanci da tsageranci a Pakistan. Tsagera masu alaka da taliban da al-Qa’ida sun dauki alhaki, su na masu fadin cewa sun kashe Bhatti ne a saboda ya nuna adawa da dokar sabo.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG