Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristoci Na Bukukuwan Kirsimeti a Duk Fadin Duniya


Wani mutum sanye da kayan Santa ya na raba kyaututtuka ga yara marasa galihu a wani yankin kasar Afrika ta Kudu. Dec. 25, 2016.
Wani mutum sanye da kayan Santa ya na raba kyaututtuka ga yara marasa galihu a wani yankin kasar Afrika ta Kudu. Dec. 25, 2016.

Kiristoci a Najeriya sun bi sahun sauran takwarosinsu na addini a duk fadin duniya wajen fara bukukuwan Kirsimeti.

A mujami’u daban daban na kasar ta najeriya an yi ta kira ga mabiya addinin na Kirista da su yi koyi da irin halayen Yesu Almasihu, wato Annabi Isa, Allah ya tabbata a gare shi.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Bishop Mike Moses, ya yi amfani da wannan lokaci wajen jaddada muhimmancin ba da kyaututtuka musamman ga mabukata.

A can Fadar Vatican kuwa, Paparoma Francis ya jagoranci addu’ar neman zaman lafiya a kasashe da ke fama da yake-yake, da kuma barazanar da ayyukan ta’addanci ke yi ga duniya.

Shugaban na mabiya darikar Katolika na duniya, ya yi misali da yakin Aleppo na Syria, tare da kira ga shugabannin kasashen duniya da su samar da mafita kan yakin.

Kiristoci ‘yan kasar Iraqi su ma sun bi sahun takwarorinsu na addini a duk fadin duniya domin yin bukuwan kirsimeti, inda su ka dunguma zuwa mujami’u a sassa daban daban na kasar.

Garin Bartella wanda a da dubban kiristoci ke zaune a cikinsa, wanda ya ke wajen garin Mosul a Lardin Nineveh, ya fada hanun ‘yan kungiyar IS a watan Agustan shekarar 2014.

Amma tun a jiya jajiberin kirsimeti aka yi ta safarar kiristoci a motocin bas-bas daga yankin Kurdawa da ke Irbil, zuwa garin na Bartella, inda a yau suka yi ta gudanar da addu’oin murnar wannan rana.

A Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justine Welby da ke jagorantar kiristoci mabiya darikar Anglika kusan miliyan 85 a duk duniya, shi ma ya yi kiran neman zaman lafiya a sassan daban-daban na duniya.

Shugaban Amurka Barack Obama da uwargidansa Michelle suna gudanar da bukuwan na kirsimeti ne a birnin Hawaii kamar yadda su ka saba tare da ‘ya’yansu Sasha da Malia.

Sannan shugaba mai jiran-gado, Donald Trump tare da uwargidansa Melania Trump a daren jiya, sun halarci wani taron addu’a a wata mujami’a da ke Florida, inda a nan ne aka daura musu aure a shekarar 2005.

Gabanin hakan, Trump ya aike a sakon Twitter na taya murnar bikin “Hanukka”, wato bikin gargajiya na Yahudawa da aka fara tun ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG