Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristan Jamhuriyar Nijer Za Su Yi Addu'ar Samun Zaman Lafiya Yayin Ayyukan Ibada Na Ista


Kiristoci a jamhuriyar Nijer

Kirista a Jamhuriyar Nijer, sun ce ba za su yarda a yi banda su ba, wajen yi wa Nijer da Najeriya addu'o'i, kamar yanda hukumomin kasar suka nemi Musulmi su yi a cikin wannan watan azumin Ramadan na bana.

La'akari da suma, sun soma azumin Ista na kwanaki 40, inda tuni suka soma nasu addu'o'in na neman samun zaman lafiya a wadannan kasashen, Kirista sun ce za su bi sahun 'yan uwansu Musulmi wajen bayar da gudunmowar tabbatar da zaman lafiya da zamantakewa mai falala.

Kirista a Jamhuriyar Nijer sun sha alwashin ba za a bar su a baya ba a wannan kasar wajen yi ma ta, da ma Najeriya addu'o'i, da hukumomin suka roka ga Musulmi a cikin wannan watan na azumin Ramadan domin kasar ta samu salama da zaman lafiya tare da makwabciyarta. Duba da yanda matsalolin tsaro suka kai wa wadannan kasashen halin intiha.

Kiristan sun ce sun soma bada umurci a Coci - Coci a wannan lokacin da suma suke yin azumin Ista na kwanaki 40, domin rokon Allah ya kawo zaman lafiya mai dorewa a Nijer da Najeriya, kamar yanda Pasto Abubakar Musa, daya daga cikin mambobin kungiyoyi na kasar Jamhuriyar Nijer na kirista ya bayyana.

Suma Musulmin kasar sun yi marhabin da jin wannan labarin, inji Liman Amadu mashawarci ga kungiyar CEDIR ta hadin kan mabambanta addinai ta gundumar Birnin N'Konni.

Samun hadin kan Musulmi da kirista a kan wannan lalura ta tsaro a kasa kamar jamhuriyar Nijer, maluman bangarorin guda biyu na cewa, ba karamin tasiri abin zai yi ba wajen samun taimakon Allah don ganin an barranta daga wannan matsalar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG