Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Koriya Ta Arewa Zuma Ce Sai Da Wuta" - In Ji Amurka


Trump da Un
Trump da Un

Yayin da duniya ke tsammanin an kama hanyar rabuwa da makamin nukiliyar Koriya Ta Arewa mai raunin tattalin arziki, sai ga shi Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo na gargadin cewa akwai sauran rina a kaba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, jiya Jumma'a, ya jaddada cewa dole ne al'ummar duniya ta matsa lamba ma Koriya Ta Arewa, muddun dai ana so ta kawo karshen shirinta na nukiliya.

"Aiwatar da tsauraran takunkumai wajibi ne ga cimma wannan buri na mu," abin da Pompeo ya gaya wa manema labarai kenan bayan jerin wasu tarurrukan gaggawa jiya Jumma'a a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York. Ya kara da cewa, "Muddun ba a aiwatar da takunkuman ba, yiwuwar Koriya Ta Arewa ta kawo karshen shirinta na nukiliya za ta dusashe."

Pompea ya yi tozali da takwaran aikinsa na Koriya Ta Ludu Kang Kyung-Wha da kuma Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres. Ya kuma yi bayani ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasar Japan game da ziyarar da ya kai Koriya Ta Arewa a farkon wannan watan, lokacin da ya samu rakiyar Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG