Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Jami'an Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast


Shugabannin Afirka kan yi taro loto-loto don samar da zaman lafiya a Nahiyar
Shugabannin Afirka kan yi taro loto-loto don samar da zaman lafiya a Nahiyar

Babban jami’in harkokin tsaron kasar Ivory Coast yace wasu ‘yan bindiga dadi ne suka hauro daga kasar Liberia suka kashe jami’an sojin kiyaye zaman lafiya

Babban jami’in harkokin tsaron kasar Ivory Coast yace wasu ‘yan bindiga dadi ne suka hauro daga kasar Liberia suka kashe jami’an sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya jiya Juma’a.

Sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya bakwai ne aka kashe a yammacin Ivory Coast. Babban jami’in harkokin tsaron Ivory Coast Paul Koffi-Koffi yana mai cewa wannan harin da‘yan bindigar suka kai ya nuna a fili cewar akwai jan aiki a gaban rundunar sojin Ivory Coast,don haka ya zama wajibi su tashi tsaye su shirya kai hare-haren tache ‘yan bindigar dake haurowa daga Liberia, makwabciyar Ivory Coast suna aikata ta’asa.

A wata takardar sanarwar da ya sanyawa hannu, jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast, Bert Koenders da kakkausan harshe ya la’anci wannan harin kwanton baunar da aka kaiwa sojin kiyaye zaman lafia na Majalisar Dinkin Duniya.

Yace Majalisar Dinkin Duniya zata dauki duk matakan da taga sun dace domin karfafa kare lafiyar sojinta masu ayyukan kare zaman lafiya.Sakatare-janar Ban Ki-moon shima ya la’anci harin tare da nuna matukar fushi da damuwa game da tsaron lafiyar sauran masu ayyukan kare zaman lafiya dake Ivory Coast.

XS
SM
MD
LG