Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Colombia Ta Nemi Gafarar Jam'iyyar Patriotic Union


Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya fito filli ya tabbatar da rawar da gwamnati ta taka wajen kashe yan jam'iyyar Patriotic Union ko UP a takaice a shekarar 1980.

Shugaba Santos ya nemi gafarar wakilan kungiyar ko kuma jam’iyar Patriotic Union da suka tsira wajen wani biki da aka yi jiya Alhamis.Yace bai kamata ace wannan bala’i ya faru ba

Sojin laima ne suka kashe kimanin mutane dubu uku a lokacin da ake shawarwarin sulhu tsakanin gwamnatin da yan jam’iyar UP a shekarar 1980, al’amarin da 'yan kasar ta Colombia suka lakawa suna kisan kiyashin siyasa.

Shugaban Santos ya gabatar da wannan jawabi ne kasa da makoni biyu kafin ya sanya hannu akan yarjejeniyar samun zaman lafiya da kungiyar Revolutionary Armed Forces of Colombia ko kuma FARC a takaice.

Yarjejeniyar zata kawo karshen yakin basasar daya kashe fiye da mutane dubu maitan da ashirin da kuma tilastawa miliyoyin mutane hasarar muhalinsu. A wani faifan vidiyo data gabtar a ranar Lahadi kungiyar FARC tace ta yi ta sace mutane cikin shekaru da suka shige, amma ba zata kara yi ba.

Tsakanin alif dari tara da saba’in zuwa shekara ta dubu biyu da goma, an sace kimamin mutane dubu ashirin da bakwai.

XS
SM
MD
LG